Home Blog

Federal Government Deepens Mining Reforms in North Central Region

0

The Honourable Minister of Solid Minerals, Dr. Dele Alake, held a strategic meeting with the North Central Development Commission (NCDC) to strengthen collaboration and unlock the vast mining potential of the North Central region.

Over 300 artisanal miners have been successfully organised into cooperatives and integrated into the formal mining system, while intensified enforcement has resulted in over 300 arrests, with multiple cases already progressing through the courts.

The administration of Bola Ahmed Tinubu continues to record tangible gains, as the value addition policy drives new processing projects and contributes over $2 billion to the economy.Sustaining momentum through collaboration and accountability.

Likitoci masu neman kwarewa sun shiga yajin aiki

0

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa wato Nigerian Association of Resident Doctors (NARD), ta sanar da fara yajin aikin gama-gari ba tare da kayyade lokacin karewa ba, bayan da gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus dinsu.Sakataren kungiyar, Shuaibu Ibrahim, ne ya bayyana hakan bayan wani taron gaggawa na kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka gudanar ta yanar gizo a ranar Asabar.Ibrahim ya bayyana matakin gwamnatin a matsayin abin takaici, yana mai zargin cewa hakan ya tilasta likitoci komawa wani sabon yajin aiki.Ya ce kwamitin ya samu bayani kan shirin gwamnati na janye tsarin alawus din, wanda ya ce ya sabawa yarjejeniyar da aka cimma a baya tsakanin bangarorin biyu.Rikicin ya samo asali ne daga yarjejeniyar da aka kulla bayan wani dogon yajin aiki da likitocin suka yi a shekarar 2025, inda aka amince da inganta albashi da alawus-alawus, ciki har da na kiran gaggawa, aikin dare, aiki a karkara da kuma wasu ayyuka marasa nasaba da jinya kai tsaye.Ko da yake an tsara fara aiwatar da sabon tsarin ne a watan Janairu na 2026, daga baya aka mayar da shi zuwa Fabrairu, kungiyar ta ce yanzu gwamnati na shirin dakatar da shi gaba daya daga watan Afrilu.

Harin Jos: Sojojin sun tsaurara bincike da sintiri

0

Sojojin da ke karkashin rundunar Operation Enduring Peace sun fara wani shiri na tsaurara bincike da sintiri a fadin birnin Jos, a jihar Plateau.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Captain Chinonso Polycarp Oteh ya fitar a ranar Asabar, ya ce an fara wannan aiki ne tun ranar Juma’a da ta gabata.

Ya ce matakin na daga cikin kokarin dawo da cikakken zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar Plateau.

Sanarwar ta ce karin jami’an tsaro da aka tura sun fara samun nasara, inda sojoji suka kama wasu mutane biyu da ake zargi, tare da kwato bindigar AK-47 da harsasai guda hudu na da kuma wata karamar bindigar.

An gudanar da wadannan samame ne a wasu wurare masu muhimmanci a Jos ta Arewa da Jos ta Kudu, ciki har da Dadinkowa, Old Airport Junction, Tudun Wada da kuma unguwar Low-cost.

Jam’iyyar ADC ta zargi INEC da yunƙurin dakatar da ita babban taron ta na Kasa

0

Jam’iyyar adawa ta ADC ta zargi hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da yunƙurin dakatar da ita daga gudanar da tarukanta domin zaɓen shugabanninta.

ADC tsagin David Mark ta yi watsi da gargaɗiin da hukumar zaɓen ƙasar ta yi, tare da jaddada aniyar ci gaba da tsare-tsarenta na gudanar da zaɓukan shugabanninta na jihohi da babban taron jam’iyyar na ƙasa.

A baya-bayan nan ne dai INEC ta gargaɗi jam’iyyar da kada ta gudanar da tarukan jam’iyyar da za su zaɓi shugabanninta don gudan Matsala har sa an warware rikicin shugabancin daya kunno kai a jamiyyar.

Cikin wata hira da gidan talbijin na Arise a ranar Juma’a shugaban hukumar Farfesa Joash Amupitan ya ce kotu ta riga ta dakatar da jam’iyyar daga gudanar da komai har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam’iyyar.Sai dai Kakakin jam’iyyar, Faisal Kabir ya shaida wa kafar BBC cewa, matakin wata ƙullalliya ce domin dana wa jam’iyyar tarko a hana ta yin tarukan ta yadda daga baya za a ce ba ta da shugabanci, don haka ba za ta shiga zaɓen 2027 ba.

Ya ƙara da cewa abin da dokokin Najeriya suka ce shi ne ka sanar da INEC taron jam’iyyarka kwana 21 kafin ranar taron, mu kuma mun riga mun sanar da ita.

CITAD Ta Tallafa wa Yara 100 da Tufafi da Kayan Karatu a Makarantar Nomadic Ta Fulani a Kano

0

CITAD ta raba tufafi da kayan karatu ga Yara 100 na makarantar firamaren Fulani ta Nomadic dake Kamanda Dan Soshiya a karamar hukumar Kiru a jihar Kano.

Wannan wani bangare ne na bunkasa fanin ilimin Yara da cibiyar ke yi a sassan kasar nan.

Da yake bayyana makasudin ziyarar, Babbban daraktan cibiyar CITAD, Dakta Yunusa Zakari Ya’u yace damuwa da halin da ilimin yara ke ciki musamman Fulani dake karkara ne ya sanya bujuro da wannan shiri.

YZ Ya’u ya kuma yi tsokaci kan yadda karancin ilimi ke sanya aikata laifukan ta’addanci tare da kira ga mahukunta da shigo don taimakawa fannin ilimin da kawo karshen matsalar.

Malam Nasiru Ibrahim Dangora shi ne Headmastan makarantar yace a kalla suna da yara kusan dari uku, sai dai har yanzu suna fama da wasu matsalolin gudanarwa.

Da yake tsokaci yayin taron, Dagacin Dangora Yusuf Harisu da ya wakilci Hakimin Kiru, ya bukaci iyayen yara su tabbatar sun tura yara makaranta tare da bibiyar su.

Malam Muhammad daya ne daga cikin iyayen yaran da ya’yansa suka fi yawa a makarantar, cikin harshen fillanci ya bayyana muhimmacin tura yara irin wadannan makarantu don samun ingattaccen Ilimi.

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin ilimin makarantar firamaren Fulani ta Nomadic na yankin Kiru wanda daga bisani CITAD ta tabbatr da cigaba da bibiyar Irn wadannan makarantu tare da tallafa musu iya karfinta.

Rundunar sojin ƙasar nan ta tura sojoji 850 Jihar Filato.

0

Shugaban rundunar sojin ƙasa na Kasar nan, Janar Waidi Shuaibu ya bada umarnin tura ƙarin sojoji 850 Jihar Filato domin tabbatar da tsaro sakamakon tashin hankalin da ya yi sanadiyar asarar rayuka a jihar.

Mai magana da yawun rundunar sojin dake aikin samar da zaman lafiya a jihar, Kaftin Chinonso Polycarp Oteh ne ya sanar da matakin, a dai dai lokacin da hukumomi ke lalubo hanyar dawo da zaman lafiya a garin Jos, bayan ƙazamin harin da ya laƙume rayukan mutane a ranar lahadin da ta gabata.

Oteh ya ce ana saran tura ƙarin sojojin ya taimaka wa waɗanda ke aiki a jihar wajen kare lafiya da kuma dukiyoyin jama’a a fadin jihar baki ɗaya.

Shugaban ya tabbatar wa dakarun cewar an tanadar musu da isassun kayan aiki da kuma haƙƙoƙin su domin ganin sun samu nasarar da ta kamata.

Kakakin rundunar sojin ya ce an É—ebo sojojin 850 daga Abuja da Kaduna domin taimakawa na Filato gudanar da aikin samar da tsaron.

za’a cigaba da sauraron shari’ar El-rufai, bayan jana’izar mahaifiyarsa.

0

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, zai sake gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna a yau domin sauraron bukatar bayar da belin sa.

An tsare El-Rufai na sama da wata guda kafin hukumar (ICPC) ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Rilwan M. Aikawa bisa tuhume-tuhume guda goma.

Zarge-zargen sun hada da mallakar kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba, karkatar da su, da kuma halasta kudaden haram (money laundering).

Tun da farko kotun ta tsayar da ranar 31 ga Maris 2026 domin sauraron bukatun da ke gaban ta, ciki har da bukatar neman belin da tsohon gwamnan ya gabatar.

Sai dai a ranar 27 ga Maris 2026, ICPC ta amince da sakin El-Rufai na wucin gadi bisa dalilai na jin kai, bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, a birnin Cairo na kasar Masar.

Ana sa ran zaman kotun zai cigaba a yau bayan kammala jana’izar marigayiyar.

An nada sanata Ibrahim Ida a matsayin shugaban hukumar yi wa kamfanoni rajista

0

An nada tsohon sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Ibrahim M. Ida, wazirin Katsina, a matsayin shugaban kwamitin gudanarwar na hukumar yi wa kamfanoni rajista Corporate Affairs Commission (CAC).

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya nada shi inda matakin ya samu yabo daga babban jami’in yin rajista kuma shugaban hukumar CAC, Hussaini Ishaq Magaji, wanda ya bayyana sanatan a matsayin wanda ya dace da mukamin.

Magaji ya ce Ida na da gogewa mai zurfi a harkokin gwamnati da kasuwanci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta ayyukan hukumar da kuma karfafa sauye-sauyen da ake aiwatarwa.

A cewarsa, nadin ya yi daidai da manufofin gwamnatin Tinubu na kawo gyare-gyare da inganta ayyukan hukumomi a karkashin shirin Renewed Hope Initiative.

Sanata Ida, wanda aka haifa a 1949, ya taba zama dan majalisar dattawa, sannan ya rike mukamin kwamishinan kudi a jihar Katsina, tare da yin aiki da gwamnati har ya kai matsayin babban sakatare kafin ritayarsa.

Ana sa ran kwarewarsa za ta taimaka wajen bunkasa ayyukan hukumar ta CAC da kuma kara inganta huldarta da sauran kamfanoni.

Wani hariin makami mai linzami ya faÉ—a kan ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza

0

Wani hariin makami mai linzami ya faɗa kan ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza, babban birnin Iraƙi.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na cewa ginin ya kama da hayaƙi, sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

Kamfanin dillacin labarai na AP ya bayar da rahoton cewa harin makami mai linzami ya faÉ—a ne kan filin da jirage masu saukar ungulu ke sauka da tashi a harabar ofishin jakadancin.

To amma kamfanin AFP ya ce jirgi maras matuƙi ya kai hari ofishin.

Harin ya auku ne jim kaɗan bayan an kashe wasu maya ƙa biyu masu goyon bayan Iran a wasu hare-hare a binrin na Bagadaza, kamar yadda AFP ya ambato wasu majiyoyi na cewa.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon tsarin fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

0

Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta bayyana wani sabon tsari na kasa mai suna One Humanitarian, One Poverty Response System (OHOPRS) da nufin fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci cikin shekaru biyar masu zuwa.

Ministan ayyukan jin kai da rage talauci, Bernard Doro, ya bayyana cewa an kirkiro shirin domin magance talauci ta fannoni da dama, ta hanyar amfani da bayanai na zamani, hadin kai da kuma tsarin da ke mayar da hankali ga jama’a.

A cewarsa a tsarin na shekarun 2026 zuwa 2030 da aka gabatar a Abuja, gwamnati na shirin tara Naira tiriliyan 16 domin aiwatar da shi.

Ya ce duk da yawan kudaden da ake kashewa wajen rage talauci, ba a samun sakamako mai gamsarwa, yana mai cewa sama da kashi 63 cikin 100 na yan Najeriya na fama da talauci mai fadi.

Ministan ya kuma ce manufar shugaban kasa, Bola Tinubu, ita ce fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci kafin shekarar 2030 tare da tabbatar da gaskiya ta hanyar fasahar zamani.

A nasa bangaren, jami’in kula da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Fall, ya ce talauci a Najeriya ya zama matsalar gaggawa.

Ya ce kashi 62 cikin 100 na ‘yan Najeriya na rayuwa cikin talauci, yayin da mutane miliyan 33 ke fama da matsanancin rashin abinci, don haka akwai bukatar sabon tsari mai hade dukkan bangarori.

Shi ma shugaban Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), Adeyemi Adeniran, ya ce kimanin mutane miliyan 133 a Najeriya na fama da talauci mai yawa bisa rahoton shekarar 2022.

Ya jaddada cewa babu wata hukuma guda da za ta iya magance matsalar talauci ita kadai, don haka akwai bukatar hadin kai tsakanin gwamnati, kungiyoyin kasa da kasa, kungiyoyin farar hula da kuma bangarori masu zaman kansu.

An tsara cewa Gwamnatin Tarayya za ta bayar da Naira tiriliyan 1.5, abokan hulda za su bayar da Naira biliyan 800, bangarori masu zaman kansu da zuba jari za su bayar da Naira biliyan 600, yayin da kudaden bangaren kasa da kasa za su bayar da biliyan 300, wanda zai kai jimillar Naira tiriliyan 3.2 a kowacce shekara.

Haka kuma, gwamnati na shirin kaddamar da Asusun Kasa na Ayyukan Jin Kai da Rage Talauci, ta hanyar sabbin hanyoyin samar da kudi kamar su kudaden yanayi, na zamantakewa, zuba jari daga kamfanoni, da kuma tsarin kudin Musulunci kamar Zakka, Sukuk da Waqf.

Domin tabbatar da gaskiya da ingantaccen tsarin gudanarwa, an samar da hanyar sa ido mai karfi da ya hada da kwamitin kasa, bangaren bincike mai zaman kansa, tsarin biyan kudi bayan samun sakamako da kuma tsarin sa ido na zamani ta hanyar fasaha.