Zulum ya ziyarci ƴan gudun hijira a jamhuriyar Nijar

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ziyarci ‘yan gudun hijrar da ambaliya ruwa ta raba da muhallansu waɗanda ke zaune a garin Bosso da ke kan iyaka da jamhuriyar Nijar.

Mutanen ‘yan asalin garin Malam-Fatori ne, shalkwatar ƙaramar hukumar Abadam da ke kusa da tafkin chadi a arewacin jihar.

Al’umar Najeriya da Nijar dai sun kwashe shekaru masu yawa suna tsallaka kan iyakar ƙasashen biyu domin cin kasuwannin da ke kan iyakar ƙasashen biyu.

Gwamnan ya ce ya je wajensu ne domin ya jajanta musu game da ambaliyar da ta shafe su, tare da alkawarta cewa gwamnatin jihar za ta taimaka musu wajen mayar da su garuruwansu da zarar ruwan ya janye.

Gwamna Zulum ya kuma gode wa jami’an ƙasar Nijar game da yadda suke tarbar mutanen jiharsa a lokutan da bala’o’i suka auku.

Article share tools

Leave a Reply