Zazzabin Lassa ya kashe mutane 178 a Najeriya a 2022

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayyana cewa an samu mutuwar mutane 178 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, sannan 989 da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa 20 ga watan Nuwamba.

Rahoton ya nuna cewa an samu mutane 103 da ake kyautata zaton sun kamu da cutar a cikin makon farkon wannan wata.

A cikin shekarar 2022, a cewar rahoton, an samu akalla mutum daya da aka tabbatar da kamuwa da cutar a fadin kananan hukumomi 107 a cikin jihohi 26, lura da cewa, daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, kashi 71 cikin 100 sun fito ne daga jihohin Ondo, Edo da kuma Bauchi.

Leave a Reply