Zanga-zanga ta ɓarke kan hare-haren ƴan bindiga a jihar Katsina

Zanga-zanga ta ɓarke a garin Ɗanmusa na Jihar Katsina bayan wani farmaki da ƴan bindiga suka kai, wanda ya yi sanadiyyar kashe mahaifiyar wani ɗan sanda da kuma ɗan’uwansa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar masu zanga-zangar sun kona gine-gine, ciki har da gidan wani tsohon malamin makaranta.

Sai dai bayanai na cewa tuni aka tura jami’an tsaro domin daƙile ƙazancewar lamarin.

Wani mazaunin garin ya ce da asubahin ranar Talata ne mahara suka shiga garin inda suka yi wa mahaifiyar ɗan sandan da ɗan’uwan nasa kisan gilla duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla da ƴan bindigar.

Katsina dai na cikin johohin Najeriya masu fama da hare-haren ƴan bindiga, waɗanda ke yin fashi da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Leave a Reply