Zan Kawo Karshen Boko Haram Gaba Daya Idan Aka Zabe Ni – Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin murkushe Boko Haram gaba daya idan har aka zabe shi ya jagoranci Najeriya a shekarar 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya bayyana hakan ne a Jihar Gombe a wajen taron yakin neman zaben jam’iyyar PDP.

Atiku ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta gina hanyoyin da za su hade yankin Arewa maso Gabas.

Atiku ya shaida wa magoya bayansa cewa gwamnatinsa za ta bunkasa harkar noma domin tabbatar da cewa wadanda ke bangaren sun samu damar yin aiki a lokacin damina da rani.

Leave a Reply