Zan cire tallafin man fetur ko za a yi zanga-zanga a Najeriya – Tinubu

Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin janye tallafin man fetur da zarar ya zama shugaban kasar.

Tinubu ya bayyana haka ne ranar Alhamis da daddare a yayin da yake gudanar da taro da wasu ‘yan kasuwar kasar.

“Dokar man fetur tana nan kuma za mu duba ta a karo na biyu domin sauke nauyin da ke kanmu kuma duk zanga-zangar da za a yi, za mu cire tallafin man fetur,” in ji Tinubu.

Ya kara da cewa: “Za mu dauki matakai masu tsauri, wannan shi ne batun gaskiya. Don haka wajibi ne mu cire tallafin man fetur.”

Ya ce ba zai ci gaba da bayar da tallafin man fetur ba saboda kasashe makwabta irin su Kamaru, Jamhuriyar Nijar, Jamhuriyar Benin ne suke cin moriyar hakan.

Tinubu ya kara da cewa zai sanya kudin da ake biyan tallafin man fetur a fannonin da suka kamata irin su lafiya.

Leave a Reply