Zan bayyana ɗan takarata na shugaban ƙasa a watan Janairu – Gwamna Wike

Gwamnan Jihar Rivers a kudancin Najeriya, Nyesom Wike, ya ce zai bayyana tare da fara yi wa ɗan takarar shugaban ƙasar da yake goyon baya yaƙin neman zaɓe a watan Janairu.

Da yake magana ranar Alhamis yayin buɗe aikin gadar sama a jihar, Wike ya ce zai jagoranci magoya bayansa zuwa jiha bayan jiha don yi wa ɗan takarar kamfe.

“Daga Janairun sabuwar shekara, zan faɗa wa mutanena wanda za su zaɓa. Saboda haka, duk mutanen da suke ta zato da kuma zagi na su jira Janairu ya zo,” in ji shi.

Tun bayan da Wike ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani na takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, aka shiga ruɗani a jam’iyyar, inda ya fara adawa da Atiku Abubakar – wanda ya kayar da shi a zaɓen.

Daga baya Wike da wasu gwamnonin PDP biyar suka kafa wani rukuni da suke kiran kan su G5 da zimmar ci gaba da adawa da Atiku, kuma suka nemi Shugaban PDP na Ƙasa Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙaminsa a matsayin sharaɗin sulhu.

Sai dai Mista Ayu ya ce ba zai sauka ba “saboda ba su suka zaɓe ni ba”.

Leave a Reply