Zamuyi duk mai yiwuwa wajen Kai Messi da Argentina Ruwa – Tata Martino

Mai horaswa na kasar Mexico Gerardo “Tata” Martino yace kungiyarsa ta kasar Mexico zasuyi duk mai yiwuwa wajen ganin sun fitar da Argentina daga gasar cin kofin duniya dake gudana a kasar Qatar.

Martino dai haifaffen kasar Argentina ne kuma tsohon kochin Messi a Barcelona a kakar wasa ta shekarar 2013/2014.

“Nasan inda aka haifeni zan kuma iya fada muku shekarar da sunan asibitin kai harma da lambar unguwar, amma zanyi iya kar iyawata naga Mexico tayi nasara a wannan wasa” inji Martino yayin zantawarsa da prematch news.

Idan dai Argentina tayi rashin nasara a wasan da zata fafata da mexico to sai dai ta koma gida don wanke riguna.

Leave a Reply