Za A Yi Amfani Da Tashar Tsandauri Ta Dala Da Ke Kano Don Rage Cinkoso A Tashoshin Legas

Ministar masana’antu, ciniki da zuba jari ta Najeriya Doris Uzoka Anite ta ce gwamnatin tarayya za ta yi amfani da tashar tsandauri ta Dala da ke Kano, saboda rage cinkoson da ake samu a tashoshin jihar Legas, da kuma kara yawan shige da ficen kayayyaki a Najeriya.

Ministar wacce ta bayyana hakan yayin wata ziyara da kai tashar da ke Kano, tace gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta mayar da hankali ne kan samar da damarmaki na ayyukan yi ga daukacin ‘yan Najeriya.

Ta kara da cewa tashar tsandaurin ta Kano za ta taimaka matuka wajen cimma nasarar farfado da tattalin arzikin kasa.

Da yake jawabi, shugaban tashar Ahmad Rabi’u ya yaba da matakin, yana mai cewa hakan zai kawo sauki ga masu samar da kayayyaki na cikin gida wajen fitar da kayan nasu zuwa kasashen ketare irin su China.

Leave a Reply