Za a sake bude makarantun firaimare da sakandire a jihar Neja
Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da shirin sake bude makarantun firaimare da sakandire da aka rufi a kananan hukumomin Rafi da Shiroro da kuma Munya saboda hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamna Abubakar Sani Bello yabbaya hakan yayin bude wasu dakunan kwanan dalibai da gidajen ma’aikata da dakunan karatu da cibiyar kashe gobara a Jami’ar Badamasi Bababngida da ke Lapai.
Ya ce za a bude makarantun ne bayan gagarumin ci gaban ta fuskar tsaron da ya shafi wadannan kananan hukumomi, ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da karfafa tsaro domin kiyaye yara ‘yan makarantar da ke yankunan.
Ya ce dakunan kwanan daliban da sauran wuraren za su rage kalubalen da dalibai ke fuskanta a jami’ar.