Za a rufe jami’o’in Najeriya saboda zaɓe
Wata sanarwa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya ta fitar ta umarci a rufe dukkanin jami’o’in ƙasar tsawon lokacin da za a gudanar da babban zaɓen ƙasar na 2023.
Sanarwar, wadda ta samu sa hannun mataimakin shugaban hukumar, mai kula da harkar gudanarwa, Chris J. Maiyaki, ta ce za a rufe jami’o’in ne domin kare lafiyar ma’aikata, da ɗalibai a tsawon lokacin zaɓen.
Bayanin ya ce umurnin ya fito ne daga ministan ilimi na Najeriyar, Adamu Adamu, inda aka umurci dukkanin shugabannin jami’o’i su rufe daga 22 ga watan Fabrairu zuwa 14 ga watan Maris.
Matasa dai na daga cikin mafiya yawa a kundin rajistar zaɓen Najeriya, kuma ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa a babban zaɓen mai zuwa.