Za A Kwashe Masu Taɓin Hankali Daga Titunan Kano

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa za ta fara kwashe masu larurar tabin hankali daga titunan jihar.

Matakin na zuwa ne yayin da korafe-korafe suka yi yawa na cewa irin wadannan mutane na gararamba a tituna, tare da barazanar cin zarafi ga kuma yanayin sanyi da ke kara tunkarowa.

Ofishin mai taimakawa gwamnan Kano kan harkokin marasa galihu da tallafawa masu karamin karfi ne ya sanar da matakin gwamnatin, na kwashe masu tabin hankalin daga tituna.

Fauziyya D. Sulaiman ita ce mai taimakawa gwamnan ta musamnan, ta ce aikin kwashe masu larurar tabin hankalin, zai fi mayar da hankali ne kan wadanda suke yawo babu kaya da masu duka.

Jami’ar ta ce an dauki aniyar wannan aiki ne don taimakon marasa galihun cikin su, wadanda da yawan su rashin kudaden zuwa asibiti ne ya kai ga tunzurar cutukansu, har suka kai ga bazuwa kan tituna.

Haka zalika matakin na da nufin dakile cutarwar da masu tabin hankalin ke yiwa jama’a a dai dai lokacin da hunturu ke karatowa.

Leave a Reply