Za a gurfanar da sojojin Ivory Coast da aka tsare a Mali a gaba kotu

A yau ne za a fara shari’ar sojojin Ivory Coast 46 da aka tsare a ƙasar Mali tun a watan Yuli a gaban kutun ɗaukaka ƙara da ke Bamako babban birnin ƙasar.

Shari’ar sojojin na zuwa ne mako guda bayan ƙasashen biyu sun amince da warware batun ta hanyar masalaha a wani tattaunawa da ƙasar Togo ke shiga tsakani.

An tsare sojojin ne dai bayan da suka isa Mali domin yin aiki da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar.

Mali dai ta zargi sojojin da yunƙurin dagula zaman lafiya da tsaron ƙasar, zargin da Ivory Coast din ta sha musantawa.

A ranar huɗu ga watan Disamba ne kuma ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta umarci shugaban mulkin sojin Mali Assimi Goita da ya saki sojojin kafin ƙarshen shekarar da muke ciki.

Leave a Reply