Za a dawo da zirga-zirgar jirgin ƙasan Abuja – Kaduna ranar Litinin

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya ta ce za ta dawo da zirga-zirgai jirgin ƙasan Abuwa zuwa Kaduna daga ranar Litinin biyar ga watan Disamba.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce jirgin farko zai bar tashar jiragen da ke Rigasa a Kaduna da misalin ƙarfe 8:00 na safe, yayin da jirgin farko da zai bar Abuja inda zai tashi daga tashar jirgin da ke Idu da ƙarfe 9:45 na safe.

Hukumar ta kuma ce daga cikin sabbin matakan tsaro da ta ɓullo da su shi ne , a yanzu wajibi ne duk fasinjan da zai hau jirgin ya nuna katinsa na shaidar zama ɗan ƙasa da kuma tikitin shiga jirgi kafin a bar su su shiga jirgin.

Idan za a iya tunawa dai hukumar sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen tsakanin biranen biyu bayan da mayaƙan Boko Haram suka kai hari kan jirgin ƙasan tare da kama fasinjoji aƙalla 60 a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna.

Leave a Reply