Yawan mutane da suke gudun hijira sakamakon yaki da sauran hatsaniya ya zarce adadin miliyan 70

yawan mutane da suke gudun hijira sakamakon yaki da sauran hatsaniya ya zarce adadin miliyan 70 a shekarar bara, adadi mafi yawa kenan da aka taba samu tun bayan da hukumar kula da yan gudun hijra ta majalisar dinkin duniya ta fara aiki kusan shekaru 70.
A rahoton da da hukumar take fitarwa duk shekara, sama da mutane miliyan 70 da digo takwas da suke fuskantar barin garuruwarsu sakamakon yaki ya karu da kaso miliyan 2.3 na mutanen idan aka kwatanta da adadin da aka fitar a shekarar data gabata.
Kazalika adadin ya ninka na shekaru ashirin da ta gabata.