Yaron da ke yaƙin ceto ‘yan uwansa daga mutuwa saboda tsananin yunwa

Yunwa ce ta yi ajalin ɗan uwan Dahir. Yanzu haka kuma akwai ‘yan uwansa mata biyu da ke kwance rai-kwakwai mutu-kwakwai saboda rashin abinci mai gina jiki.

Wakilin BBC Andrew Harding ya koma Baidoa domin sake ziyartar iyalan da fari ya raba da matsugunansu irin sa mafi tsanani a cikin shekaru 40 a Somalia, yayin da mahukunta ke kira ga ƙasashen duniya su ayyana dokar ta-baci kan yanayin da ake ciki a ƙasar.

Gargadi: Wannan makala na dauke da hotunan da ka iya tayar da hankalin mai karatu

Dahir, mai shekara 11, yana ratsawa tsakanin bukkoki da ke gefen dajin Baidoa, zuwa ga makarantarsu ta kwano da aka gina a kusa da wata babbar hanya.

Leave a Reply