Iyaye a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, na ci gaba da kokawa dangane da rashin sanin ranar da ‘ya’yansu dake makarantun firamare dake jihar zasu rubuta jarabawar shiga makarantar sakandare wato common entrance a turance.
Iyayen na wannan koke ne yayin da aka shiga mako na uku da komawa sabon zangon karatu na bana a Kano, ba tare da sanin makomar ‘ya’yansu da yanzu ake musu kallon ‘yan Aji bakwai ba.
Ko da BBC ta kai ziyara wata makarantar firamare da ke Kanon don jin ta bakin daliban da suke aji shida, daliban sun shaida cewa sun kasance a aji bakwai ne saboda rashin rubuta jarrabawar kamala firamare.
Daliban sun ce duk lokacin da suka tambayi shugaban makarantarsu wato hedimasta, sai ya ce musu zaku ji kira a rediyo.