Yara biliyan 1.4 na rayuwa cikin matsanancin talauci a duniya – Majalisar Dinkin Duniya

Wani rahoto daga Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa a kalla yara biliyan ɗaya da miliyan ɗari huɗu ƴan ƙasa da shekaru 16 ne a fadin duniya suka gaza samun kowanne irin tallafin kariya na zamantakewar al’umma.

Kasa da kashi 10 cikin 100 na yara da ke kasashe masu karamin karfi ne suke samun tallafin da ya kamata yara su samu, yanayin da ke jefa su cikin hadarin kamuwa da cututtuka da karancin ilimi da kuma talauci.

Rahoton yace wannan yanayin ya jefa yaran cikin mawuyacin hali sakamakon fuskantar cututtuka da rashin abinci mai gina jiki da kuma tsananin talauci.

Kungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO) da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da kungiyar Save the Children ne suka tattaro wadannan bayanan.

A ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi, ƙasa da kaso 10 cikin 100 na yara ne ke samun tallafin da ya kamata su samu, yanayin da ke nuna gagarumin bambancin da ke tsakani idan aka kwatanta da damarmakin da yara waɗanda ke ƙasashe masu arziki suke samu.

Darakta a sashen da ke kula da tsare-tsare da kuma samar wa al’umma kariya na UNICEF Natalia Winder Rossi, tace faɗaɗa ayyukan samar da kariya ga yara a yaƙin da ake yi da talauci yana da matuƙar muhimmaci, gami da samar da ci gaban kowanne yaro a duniya.

Haka kuma kungiyoyin sun ce tallafa wa yara na da matuƙar muhimmaci wajen samar musu kariyar da ake da niyyar yi don inganta rayuwarsu na tsawon lokaci.

Leave a Reply