‘Yansandan Najeriya sun cafke mutane 245 a cikin mako 2 kan zargin aikata laifi

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta sanar da cewa; tayi nasarar cafke mutum 99 da ake zargi da aikata laifin fashi da makami da wasu mutum 153 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kubutar da mutum 35 daga hannun wadanda suka yi garkuwar da su a cikin mako 2 a wani samame da jami’anta suka kai a sassan kasar.

‘Yansandan sun kuma ce sun kama motocin sata, da cafke wasu ‘yan kungiyar asiri mutum 9 da bundugu 44 da alburusai 477.

Kakakin Rundunar na kasa, Olumuyiwa Adejobi, shine ya bayyana hakan yayin wani taron manaima labarai a Shelikwatar rundunar dake Abuja.

Daga; Idris Usman Alhassan Rijiyar Lemo da Murtala Shehu Abubakar

Leave a Reply