‘Yan wasan Premier za su saka baƙin kambi don tunawa da Pele

Ƙungiyoyin Premier League da na gasar kofin ƙalubale na shirin sanya baƙin kambi tare da tafi na minti ɗaya domin nuna girmamawa ga fitaccen ɗan wasan Brazil Pele da ya mutu ranar Alhamis.

Ɗan wasan wanda ya lashe kofin duniya sau uku ya mutu ne yana da shekara 82.

Ana ci gaba da bayyana alhini tare da miƙa saƙon ta’aziyya kan rasuwar tsohon ɗan ƙwallon.

Brazil ta ayyana hutun kwana uku a ƙasar domin yin maƙoƙin rasuwar tsohon ɗan wasan.

Za a fara wasan mako na 17 a gasar Premier ranar Juma’a da wasanni biyu, inda za a ƙarƙare wasannin makon ranar Lahadi, inda ‘yan wasan za su tuna da tsohon ɗan wasan a duka wasannin 10.

Hukumar shirya gasar kofin ƙalubale ta ƙasar ta ce za a yi tafi na minti ɗaya a wasannin ranar Juma’a, da na ranar Lahadi da Litinin, yayin da ‘yan wasan za su saka baƙin kambi domin tunawa da Pele.

Leave a Reply