‘Yan sanda sun kama kwamandan IPOB da ya jagorancin kisan Ahmed Gulak

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta yi holen wani kwamandan IPOB da ta daɗe tana nema ruwa a jallo mai suna Chinwendu Nwangwu wanda aka fi sani da Onyearmy bayan da ta samu nasarar kama shi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Michael Abattam, ya ce an kama mista Nwaagwu wanda ya bar aiki a rundunar sojin Najeriya shekara takwas da suka gabata a yankin ƙaramar hukumar Aboh Mbaise da ke jihar.

Mista Abattam ya ce tsohon sojan mai shekara 34 ya aikata laifuka da dama ciki har da kashe-kashen mutane, da kai hare-hare ofisoshin zaɓe a jihar.

Rundunar ‘yan sanadn jihar ta ce bayan da ta binciki gidansa ta samu bindigogi biyar, da wasu manyan bindigogin, da ƙananan bindigogi ƙirar gida, da gidan alburusai 50, da gurneti tara ƙirar gida.

Haka kuma mista Nwangwu ya amsa laifin bai wa jami’an ƙungiyar ‘yan aware da ESN kusan 1,000 horon makamai da dabarun harin ta’addanci.

Sannan kuma mista Onyearmy ya amince cewa ya jagoranci hare-hare da dama a jihar musamman kan jami’an tsaro da ofisoshin ‘yan sanda da na hukumar zaɓe a jihar.

Ya kuma bayyana yadda ya shirya harin da ya yi sanadin mutuwar Ahmed Gulak, mai bai wa tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan kan harkokin siyasa.

Leave a Reply