‘Yan sanda sun kama fitaccen dan bindiga a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta kama fitaccen ɗan bindiga Bilyaminu Sa’idu a ƙaramar hukumar Zariya.

Kakakin rundunar, DSP Mohammed Jalige, ya ce ‘yan sandan da ke aiki a yankin Tudun Wada Zariya ne suka kama ɗan bindigar yayin da suke samame a Kwarkwaron Manu yankin Basawa inda suka tare wasu mutum biyu a kan babur da ba shi da lamba.

Ya ƙara da cewa mutanen suna ɗauke da wasu jakunkuna da ake zargin an ɓoye bindigogi.

Bayan an tare su ne, sai ɗaya daga cikinsu ya yi yunƙurin tserewa lamarin da ya sa aka kama shi.

An gano bindigogi kirar AK47, da harsasai dari uku da arba’in da wayoyin salula goma da kuma magunguna a cikin jakar.

Leave a Reply