“Yan Nijeria kimanin dubu 14 da 35 ne suka dawo Kasarnan daga Libya” NEMA

Hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa NEMA ta sanar da cewa ‘yan nijeria kimanin dubu 14 da 35 ne suka dawo Kasarnan daga Libya bisa radin kansu.

‘yan nijeriyan wadanda suka kasance a cikin wani yanayi na zaman dabaro a Kasashen Libya da Mali da Burkina Fasao da Faransa da Ireland da makamantansu, sun dawo Kasarnan ne bisa jagorancin hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta duniya da kuma kungiyar tarayyar Turai.

Shugaban hukumar ta NEMA dake ofishin filin hawa da saukar jirage dake Legas ne ya sanar da hakan, inda yace baya ga wadannan akwai ‘yan gudun hijran Kasarnan 137 da suka dawo kasarnan a ranar alhamis.