YAN NAJERIYA NA NEMAN MAFAKA A JAMHURIYAR NIJAR

Kimanin yan kasar nan dubu 23 ne ke neman mafaka a jamhuriyar  Nijar sakamakon tashe tashen hankulan da suke fama da su a yankin arewa maso yamma na kasar nan.

Maimagana da yawun babban kwamishinan kula da yan gudun hijira na Majalissar dinkin duniya Mista Babar Baloch ne ya sanar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Geneva.

Yace akwai sama da yan gudun hijira sama da dubu 60 dake neman mafaka a jamhuriyar Nijar daga watan Afrilun shekarar da ta gabata zuwa yanzu.

Hukumar kula da yan gudun hijira ta majalissar dinkin duniya ta nuna bukatar ta ta samun wadataccen zaman lafiya a kasar nan da kuma kawo karshen barazanar da sojin Nijar ke fuskata.

Idan ba amanta ba dai tun a farko farkon shekarar da ta gabata ta 2019 ne al’ummar jihohin Katsina , Sokoto da Zamfara ke fama da hare haren yan bindiga dadi.