‘Yan Majalisun Najeriya Sun Bukaci A Koma Tsarin Mulki Na Firaminista

Wasu ‘yan majalisun tarayyar Najeriya sun bukaci kasar da tayi watsi da tsarin mulkin shugaban kasa mai cikakken iko tare da komawa tsarin mulki irin na Firaminista kamar yadda aka yi a Jamhuriyar ta farko, domin juya akalar kudaden da ake kashewa wajen yiwa talakawa aiki.

A karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ‘yan majalisar wakilai 60 da suka gabatar da bukatar a shirin yiwa kundin tsarin mulki garambawul, sun ce suna matukar damuwa da irin makudan kudaden dake tafiya bangaren zartarwa, da kuma karfin fada a ji da shugaban kasa mai cikakken iko ke da shi a karkashin wannan tsarin.

Kazalika sun ce a baya duk kokarin da majalisun tarayya suka yi wajen rage kudaden da ake kashewa bangaren shugaban kasar da kuma ragewa shugaban karfin fada a ji ya ci tura saboda masu cin gajiyar tsarin.

‘Yan majalisar sun kara da cewa duk da yake wannan gyara ne da zai dauki dogon lokaci da kuma bukatar wayar da kan jama’ar kasa domin goyan bayan tsarin, suna da yakinin cewar ko da ba a samu biyan bukata a karkashin wannan majalisa ba, ana iya samu a majalisar da za ta biyo bayan ta.

Leave a Reply