‘Yan majalisa sun bukaci a kawo fashi da rashin tsaro a Katsina

  Majalisar wakilai ta Taraiya ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya daina nuna tsausayi wajen yakar aiyukan ta’addanci na wasu ‘yan Najeriya da suka addabi jihar Katsina.

Wannan na zuwa ne bayan wasu mabanbantan hare-hare da ‘yan bindiga suka kai wasu sassan jihar kamar yadda bayanan baya-bayan nan suka tabbatar.

Amincewar na zuwa ne sakamakon wani kudirin gaggawa da wakilin kana nan hukumomin Jibia da Kaita daga jihar Katsina, Sada Soli ya gabatar a yayin zaman majalisar.

Da yake jawabi ga takwarorinsa na majalisar yayin gabatar da kudirin, dan majalisar ya nuna damuwa kan karuwar kashe-kashen rayukan mutane da barnata dukiyoyin su a shiyyar Arewa maso yamma tare da kiran a gaggauta daukar matakin magance matsalar tun daga tushe.

Daga; Idris Usman Alhassan Rijiyar Lemo da Murtala Shehu Abubakar

Leave a Reply