‘Yan Majalisa 27 Sun Fice Daga PDP da Wasu Jam’iyyu Zuwa APC, ADC da Sauransu

An samu yawaitar masu sauya sheƙa a Majalisar Wakilai ta Tarayya, inda jam’iyyun ADC, APC da wasu suka samu ƙarin mambobi, yayin da ‘yan siyasa ke ƙara sauya matsayi gabanin zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta sanarwar sauya sheƙar a zaman majalisa na ranar Talata.

Jimillar ‘yan majalisa 27 ne suka sauya sheƙa a wannan karo, wanda ake ganin yana daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa a majalisar, ƙasa da shekara guda kafin ‘yan Najeriya su sake zuwa rumfunan zaɓe domin zaɓar shugabanninsu.

Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar, mutum 14 sun koma jam’iyyar APC.

Sannan mutum 8 sun koma jam’iyyar ADC, waɗanda suka haɗa da ‘yan majalisa 5 daga PDP, 2 daga LP, da kuma 1 daga APC. A gefe guda kuma, jam’iyyar APP ta samu ‘yan majalisa 2, ɗaya daga PDP da ɗaya daga LP.

Haka zalika jam’iyyar Accord Party ta samu sababbin ‘yan majalisa 2 daga PDP, wanda hakan ya ƙara ƙarfin jam’iyyar, wacce ke mulki a jihar Osun.

‘Yan majalisar sun bayyana cewa sun sauya sheƙa ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyunsu na baya.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka sauya sheƙa sun haɗa da:

Aliyu Madaki – daga NNPP zuwa APC (Dala, Kano)

Tijjani Abdulkadir Jobe – daga NNPP zuwa APC (Kano)

Ghali Tijjani Mustapha – daga NNPP zuwa APC (Kano)

Shehu Bello – daga NNPP zuwa APC (Kano)

Dankawu Idris – daga NNPP zuwa APC (Kano)

Hussain Hassan Shehu – daga NNPP zuwa APC (Kano)

Rabiu Yusuf – daga NNPP zuwa APC (Kano)

Garba Mohammed Chiroma – daga NNPP zuwa APC (Kano)

Ibrahim Mohammed – daga NNPP zuwa APC (Kano)

Sauran sun haɗa da: Jaafaru Yakubu – daga PDP zuwa APC (Taraba)

Sadiq Abbas Tafida – daga PDP zuwa APC (Taraba)

Bello Shinkafi – daga PDP zuwa APC (Zamfara)

Yaya Bauchi Tongo – daga PDP zuwa ADC (Gombe)

Umar Yusuf Yabo – daga PDP zuwa ADC (Sokoto)

Haka kuma akwai wasu da suka koma jam’iyyun APP da Accord daga PDP da LP a jihohin Imo da Osun.

Masu sharhi na ganin cewa wannan sauya sheƙa na nuna yadda siyasar Najeriya ke shiga sabon yanayi na sake fasali, yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Latest news
Related news

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here