‘Yan Fashin Daji Sunyi Karkuwa Da Mahaifiyar Mawaki Dauda Kahutu Rara

Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Katsina ta ce ta kama mutum biyu bisa zargin su da hannu a garkuwa da mahaifiyar wani fitaccen mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.

A tattaunawarsa da BBC, Mai magana da yawun rundunar a Katsina, Sadiq Hikima ya ce “muna tsare da mutum biyu kan lamarin, muna ci gaba da bincike”.

Tun farko, kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Nasiru Mu’azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma’a a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja.

Mu’azu ya ce waɗanda suka sace matar sun yi hakan ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami’an da ke tsaron gidan sun sani ba.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami’an tsaro waɗanda suka bazama cikin dazuka domin bin sawun ƴan bindigan

Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fuskantar matsalar tsaro, inda ƴan bindiga ke kashewa tare da yin garkuwa da mutane.

Hakan ya durƙusar da sana’o’i da harkoki na yau da kullum.

Leave a Reply