‘Yan fashin daji sun hallaka mutum 21 a jihar Bauchi

Daga jihar Bauchi kuwa, ‘yan fashin daji sun hallaka mutane 17 a kauyen Rimi dake kusa da dajin shakatawa na Yankari a karamar hukumar Alkaleri a jihar.

Dubban mutane da suka hadar da mata, kananan yara da dattawa sun fara kauracewa gidajensu sakamakon hare-haren da ‘yan fashin dajin suka kai wasu kauyuka na karamar hukumar.

Bincike ya nunar da cewa an samu yawaitar aiyukan masu hakar ma’adanai a wasu kauyuka, wanda aka ja hankalin masu hakar ma’adanan a karamar hukumar Alkaleri da suyi taka-tsan-tsan sakamakon karuwar aiyukan ‘yanfashin daji.

A nata bangaren Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, ta musanta rohoton kai harin da karkashe mutane a karamar hukumar ta Alkaleri.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ta Bauchi, Sp Muhammed Wakili, yace babu wani hari ko kisan mutane a sabuwar matatar man da aka gano a wasu yankuna na jihar ta Bauchi.

Leave a Reply