‘Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Benue

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benue.

Mazauna ƙauyen sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a Tse Fela da ke Mbabuande da Tse Akyegh da ke yankin Ikaaghev.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa al’ummar yankin lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana, inda maharan suka afka wa gidaje da muggan makamai tare da kashe mutane da kuma raunata wasu.

Shugaban karamar hukumar Gwer West, Andrew Ayande, ya tabbatar da cewa an kashe mutane bakwai a harin da aka kai wa al’ummomin biyu.

Ayande ya ce ci harin ya tilasta wa mutanen ƙauyen barin garuruwan da suke tun daga ranar Talata zuwa Laraba.

Sai dai mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Benue, SP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu wani rahoto kan lamarin ba.

Leave a Reply