YAN BINDIGA SUN HALLAKA MUTANE A JIHAR KATSINA

Sama da mutane 20 ne suka rasa rayukan su a hare haren da wasu yan bindiga dadi suka kai jihar Katsina.

Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace yan bindindigan sun kai haree haren ne a kananan hukumomi 4 dake jihar, wato Karamar hukumar Batsari, Dutsinma, Faskari da kuma Safana, in da kuma suka yi garkuwa da mutane 4 baya ga hallaka wasu mutanen.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun isa kananan hukumomin ne a babur in da suka fara harbe harbe lokacin da suke kara shiga cikin mutanen.

Yan bindigar sun hallaka mutane a kauyukan Dan Jukka da Salihawar Kalgo a karamar hukumar Safana kuma suka kashe mutane 5, sai kuma Unguwar Buntu, Gidan Baki da kuma Dogon Awo a karamar hukumar Faskari inm da nan ma suka hallaka wasu mutanen.