Yakamat a rika baiwa mata mukamin mataimakin gwamana a arewacin Najeriya – Aisha Buhari

Uwargidar shugaban ƙasar Najeriya, A’isha Buhari ta buƙaci shugabanni a arewa su yi koyi da na kudancin ƙasar wajen naɗa mata a muƙamin mataimakan gwamnoni.

Hajiya A’isha ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa ta kafar sada zumunta, inda ta ce naɗa matan a muƙamin zai taimaka wajen shigar da su a harkar siyasa.

Ta ƙara da cewa “wannan ce hanya mafi kyawu a ƙoƙarin ganin an yi adalci ta ɓangaren jinsi, a maimakon goyon bayan mutum guda mai neman nasara ko ta halin ƙaƙa.”

A cikin sanarwar tata, A’isha Buhari ta kuma gode wa jagororin jam’iyyar APC na jihar Adamawa, inda rikici ya turnuƙe a kan takarar gwamnan jihar.

A makon da ya gabata ne kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa Sanata A’isha Binani ce halastacciyar ƴar takarar gwamna, bayan wata kotun ta soke takarar.

Leave a Reply