Yadda muka gano likitocin bogi 199 – Gwamnatin Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, Muhammad Bello Matawalle, ya ce gwamnatin jihar ta gano sunayen likitocin bogi kimanin 199, waɗanda ake biyan albashi a jihar.
Gwamna Matawalle na wannan jawabi ne a wani taron manema labarai a hedikwatar ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar.
Matakin na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake kokawa game da karancin likitoci a cibiyoyin kula da lafiya na matakin jiha da gwamnatin tarayya.
A cewar gwamnan yayin da gwamnatin jihar ke biyan likitoci 280 albashi a jihar a duk wata, ta gano cewa likitoci 81 ne kawai ke aiki a jihar.
Gwamnan ya ƙara da cewa tuni ya zanta da ƙungiyar kwadago ta ƙasa domin gano waɗannan likitoci 199, da suka kwashe tsawon lokaci suna karɓar albashi alhalin ba sa yi wa gwamnatin jihar aiki.
Ya kuma ce akwai bukatar a gano waɗanda ke da hannu a wannan cuwa-cuwa.
Matawalle ya ce an gano waɗannan sunaye ne sakamakon aikin tantance ma’aikata da gwamnatin jihar ke gudanarwa ƙarƙashin ofishin shugaban ma’aikata na jihar, a wani bangare na kokarin da gwamnatin ke yi na fara aiwatar da tsarin biyan albashi mafi kankanta na N30,000.
Ba za mu rage yawan ma’aikatanmu ba
Gwamna Matawalle ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta rage ma’aikata ba kan batun aiwatar da mafi karancin albashin.
“Ba zan kori ko wane ma’aikaci ba da yake yi wa gwamnati aiki. Maganar gaskiya ma na gina gidaje 450 domin ma’aikatan jihar nan kuma zan mika gidajen garesu ranar Lahadi,”
“Amma za mu tsaftace ma’aikatunmu bisa tafarkin doka domin bada damar fara biyan N30,000 a matsayin albashi mafi kankanta,” in ji shi.
Gwamna Matawalle ya kuma ce gwamnatinsa za ta rubanya kokarin da take yi domin inganta harkar kiwon lafiya ga duk yan jihar, matukar aka sake zabensa a karo na biyu.
Ko a shekarar 2019 ma, Gwamnatin Zamfara ta ce za ta gurfanar da ma’aikatan da ta gano suna karbar albashi fiye da daya a gaban kotu, bayan ta kaddamar da bincike domin gano ma’aikatan bogi.
Matsalar likitocin bogi ta dade ana fama da ita a matakin jihohi da gwamnatin tarayya.
Masana sun alakanta yadda ake samun zirarewar kudaden gwamnati ga matsalar ma’aikatan bogi.