Yadda ake samun ƙaruwar mata da ba sa samun abinci su koshi a Najeriya

Adadin ‘yan mata da matan da ba sa samun isasshen abinci, su ci, su koshi, ya ƙaru zuwa sama da miliyan bakwai a Najeriya.

Wani rahoto da Asusun kula da kananan yara na Duniya UNICEF ya fitar, ya kuma ce fiye da rabin ‘yan mata da mata a Najeriya wato kashi 55 cikin 100 suna fama da matsalar karancin jini.

Rahoton wanda ke zuwa daidai lokacin da ake bikin ranar mata ta duniya a yau, ya ce kusan rabin matan da ke cikin shekarun haihuwa a Najeriyar ba sa samun lafiyayyen abinci mai gina jiki.

Abin da rahoton UNICEF ya kunsa

Rahoton na UNICEF ya ce wani ƙiyasi na Gidauniyar Cadre Harmonise da gwamnati ta wallafa a bara ya nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 17 ne ke fama da matsananciyar yunwa, kuma akwai yiwuwar adadin zai karu zuwa miliyan 25 idan an shiga tsakiyar damunar bana.

Ya ce ‘yan mata da matan Najeriya ‘yan shekara 15 zuwa 49 da ba sa samun isasshen abinci, ya karu ne daga adadin miliyan biyar da dubu 600 a 2018 zuwa adadin mata miliyan bakwai da dubu 300 a 2021.

A cewar UNICEF matsalar kuma ta ta’azzara ne saboda annobar korona da yaƙin Ukraine da farin da ake ci gaba da fama da shi da rikice-rikice da kuma rashin kwanciyar hankali a wasu sassa.

Rahoton ya ce ‘yan mata da matan da ke fama da karancin jini a Najeriya saboda ba sa samun abincin da masana ke ba da shawara na aƙalla biyar cikin rukunonin abinci goma kamar hatsi da dangin doya da wake da kayan marmari da nono da nama da kaji da kifi da kwai da kayan lambu da sauran abinci dangin bitamin A, da ake samu a cikin kayan marmari da kayan lambu.

Ya ce karancin abinci mai gina jiki a rayuwar mata da ‘yan mata na iya janyo musu raunin garkuwar jiki da raunin kaifin fahimta da karin hatsarin fuskantar larurori masu barazana ga rayuwa ciki har da a lokacin goyon ciki da haihuwa, abin da ke sanya rayukan mata cikin kasada.

A cewar UNICEF ga misali a Najeriya, kananan yara miliyan 12 ‘yan ƙasa da shekara biyar suna fama da tsumburewa, a cikinsu kuma kusan rabi sun gamu da tsumburewar ne a lokacin da suke cikin iyayensu da kuma a wata shida na farkon rayuwarsu, wato gaba ɗaya adadin kwana 500 lokacin da yaro kacokam ya dogara da abincin da mahaifiyarsa ke ci.

Tun a bara, in ji rahoton, UNICEF ya ƙara kokari a kasashen da suka fi fama da matsalar karancin abinci a duniya ciki har da Najeriya ta hanyar wani shiri na gaggawai don karewa, da ganowa da kuma kula da lafiyar mata da kananan yara da ke fama da rama

Type 

Leave a Reply