Ya kamata a Yan Sanda su kama Shugaban APC na Kano – Abba Gida-gida

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar adawa ta NNPP, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kira da a gaggauta kama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, tare da gurfanar da shi gaban kuliya bisa zarginsa da neman tada zaune tsaye da kuma tunzura al’ummar jihar kano.

 A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun da mai magana da yawun dan takarar gwamnan na jam’iyyar NNPP  Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aikewa manaima labarai, yace Abba Yusuf ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar nan da su gaggauta daukar mataki ta hanyar kame Abdullahi Abbas domin dakile tashe-tashen hankula a siyasar Kano da kuma kare rayuka da al’umma.

Leave a Reply