Wike Ya Ba Shugaban Ƙasar Sanigal Bassirou Faye Shaidar Zama Ɗan Ƙasa A Abuja

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye shaidar girmamawa na zama dan kasa a Abuja.

Wike ya karrama shugaban na Senegal ne lokacin da ya tarbe shi a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a madadin shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya ce, shaidar za ta bai wa shugaban kasar Senegal dukkan hakkoki da ‘yanci na dan kasa a babban birnin tarayya Abuja.
Haka kuma za ta kasance wata alamar girmamawa da karfafa abota da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Senegal.
An ruwaito cewa shugaba Faye na Senegal ya iso Najeriya ne domin ganawa da shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar raya arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS.

Leave a Reply