Wata tanka mai dauke da man dizel ta fashe a kan titin Rano

Wata tanka mai dauke da man dizel ta fashe a kan titin Rano dake karamar hukumar Bunkure abinda yayi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wani guda.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano,Sa;idu Muhd ya fadawa yan jarida cewa hadarin ya faru ne da safiyar jiya, alhamis.

Yace basu iya gano lambar motar ba sakamakon wutar data tashi.

Ya kuma danganta hadarin da gudun wuce sa’a wanda acewar shi, hakanne ya sa motar ta subucewa direban.

Acewar Sa’idu Muhd, mutane biyu ne al’amarin ya shafa kuma daga cikinsu, daya ya rasu yayinda dayan kuma ya samu rauni.