Wata Babbar Kotun Taraiya ta yankewa Tsohon shugaban jami’ar Gusau hukuncin ɗaurin shekaru 35

Wata babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke wa tsohon shugaban jami’ar tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba hukuncin ɗaurin shekara 35 a gidan yari.

Mai shari’a Maryam Hassan Aliyu, wadda ta yanke hukuncin ta ce an samu farfesa Garba ne da laifuka biyar da suka jiɓanci amfani da ƙarya wajen karɓar kuɗi da kuma zamba.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar gaban kotu a ranar 12 ga watan Oktoba kan zargin sa da tatsar kuɗi daga wani mutum bisa alƙawarin ba shi kwangilar katange jami’ar, wadda kuɗinta ya kai naira biliyan uku.

A lokacin da ta yanke hukunci, mai shari’ar ta ce ta gamsu da bayanan da EFCC ta gabatar, sannan ta yanke masa hukuncin jimillar shekaru 35 a gidan maza.

Leave a Reply