Wasu mutane sun kai wa mijin kakakin wakilan Amurka  hari.

An garzaya da mijin Shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi asibiti, bayan wasu mutane sun kutsa kai gidansa.

Rahotanni sun ce mutanen sun raunata Paul Pelosi mai shekara 82 a gidan nasa da ke San Francisco da safiyar yau.

To amma jami’an tsaro sun yi nasarar kama su, duk da kawo yanzu ba a san dalilinsu na afka masa ba.

Mai magana da yawun iyalin Mr Pelosi ya ce yana samun sauki kuma suna fatan zai warke sarai.

Leave a Reply