Wasu jami’an gwamnatin Najeriya na da hannu kan badakkalar naira tiriliyan 89 – Gudaji Kazaure

A Najeriya, wani kwamiti na musamman da shugaban kasar ya kafa domin ya gudunar da bincike a kan cajin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna kokarin hana shi yin aikin sa, da kuma hana shi ya mika wa shugaba Buhari rahotonsa.

Kwamitin wanda aka dora masa alhakin binciken cajin kudin ajiya da cire kudin tun daga shekara ta 2013 zuwa yanzu ya gano cewa babban bankin kasar ya tara fiye da naira tiriliyon tamanin, amma ya yi zargin cewa ana sama da fadi da kudin.

Muhammad Gudaji Kazaure, shi ne sakataren kwamitin kuma ya shaida wa BBC cewa kwamitin shugaban kasar ya gano wasu makudan kudade:

“Kwamitinmu ya gano naira tiriliyan 3.9, kuma yayi kokarin shiga babban bankin Najeriya domin gano inda wadannan kudaden suke cikin asusun ajiya guda uku.”

Ya ce akwai naira biliyan 171 na cikin asususn ajiya na farko zuwa shekarar 2020, kuma akwai bashin naira tiriliyan 23.4 da aka ba bankuna, kuma akwai bashi da ake ranta wa gwamnati na tiriliyan 13.

“Ta ina aka samu wadannan kudaden. Kudin gwamnati ne ake ranta wa gwamnati?”

Ya tuhumi cewa kudaden da bankunan Najeriya naira dari-dari ne aka tara har aka sami wadannan tiriliyoyin kudaden na shekaru hudu zuwa shida.

“Kudi ne da ba a sakawa cikin asusun ajiyar gwamnati – daga asusun ajiya mallakin wasu mutane ake tura su asusun masu zuba jari (investors account), shi ke nan sun zama mallakinsu,” inji shi.

Gudaji Kazaure ya kuma ce ana yi musu nuku-nuku kan binciken da shugaban kasa ya bukaci su yi.

“Shi gwamnan babban banki da alkalin alkalai hankulansu sun tashi da na fara wannan bincike, haka ma ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati.”

Leave a Reply