Babban Sufetan ‘yan sandan kasarnan ,Usman Baba Alkali ,ya musanta rade-radin da ke yawo cewa ,rundunartasu na shirin dawo da sashen dake yaki da fashi da makami na SARS ,bayan rusheshi da akayi a shekarar data gabata .
An dai rushe sashen na SARS mai yaki da ayyukan fashi ne a watan Oktoban shekarar 2020, bayan tarzomar #EndSARS da aka gudanar a sassa daban-daban na kasar nan.
Rahotanni sun bayyana cewa tuni aka fara shirye-shiryen dawo da SARS, shekara guda bayan rushe ta da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi.
Sai dai shugaban ’yan sanda, cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sanda na kasarnan Frank Mba, ya fitar ya musanta rahotannin.
Ya bayyana cewa Hukumar ‘Yan Sandan ta samu labarin wasu rahotanni da ke ta yawo cewa ana shirin dawo da rundunar ta SARS ,In da ya kara da cewa babu wani abu mai kama da hakan, an rusherundunar ta SARS kuma sun tafi ke nan babu wani abu da zai sa su sake dawowa.
Daga bisani y ace sun gama shirye-shiryen yadda sabuwar tawagar ’yan sanda za su fara aiki don maye gurbin da SARS tabari, ya kuma yi kira hadi da jan hankalin jama’a da su yi watsi da wannan labari wanda babu gaskiya a cikinsa.