UNICEF ta nuna damuwarta kan garkuwa da yara 21 da aka yi a jihar Katsina
Hukumar “UNICEF ta damu da rahoton sace yara a kalla 21 a wata gona a unguwar Mairuwa, dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, arewa maso yammacin Najeriya.”
Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate, c eta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar, inda “Rahotanni suka tabbatar da cewa ‘yan bindiga ne suka sace yaran 21 – ‘yan mata 17 da maza 4 – masu shekaru tsakanin 15 zuwa 18, an sace su ne a ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 12:30 na rana.
Ta kara da cewa “Sace yara ko a gida, a makaranta, a gona, ko a wani wuri, abin takaici ne dake bukatar daukin gaggawa. Satar Yara ya zama abin tashin hankali, musamman ga wanda ya kamata ya ba su kariya.
UNICEF “tayi kira ga hukumomi da su dauki matakin da ya dace don kubutar da yaran da aka sace tare da hada su da iyalansu ba tare da bata lokaci ba.”
“UNICEF ta kuma yi kira ga hukumomi da su kubutar da sauran mutanen da aka ruwaito an yi garkuwa da su a gona a daidai lokacin da aka sace yaran.”