Ukraine ta shiga sabuwar shekara da luguden hare-hare daga Rasha

Rahotanni daga Ukraine na cewa an ji yo ƙarar tashin wasu hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kai a Kyiv, babban birnin ƙasar.

Shugaban rundunar sojin Ukraine ya ce sun yi nasarar harbo makamai 12 cikin 20 da aka harba ƙasar.

Shugaba Volodymyr Zelensky a wani jawabi da ya gabatar, ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da yaƙi har sai ta yi galaba.

Ya kuma zargi Rasha da biyewa huɗubar Shaiɗan ganin irin hare-haren da take kai wa kan farar hula a ranakun Kirsimeti da sabuwar shekara.

A Rasha kuwa, Shugaba Putin ya gabatar da jawabinsa na sabuwar shekara ga ƴan ƙasar ta Talabijin inda aka nuna shi yana faɗa wa sojojinsa cewa suke da nasara.

Leave a Reply