Ubangidan ƴan siyasar da zai jagoranci Najeriya

An ayyana Bola Tinubu, mai shekara 70 a duniya a matsayin mutumin da ya ci zaɓen Najeriya mafi zafi tun bayan mulkin sojoji a 1999.

Tinubu, wanda ake kallo a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa da ya kawo ci-gaba a jihar Legas – cibiyar kasuwancin ƙasar, ya yi nasara ne kan babbar Jam’iyyar hamayya mai fama da ɓaraka da kuma ɗan takara na uku da ke da magoya bayan matasa.

A ranar 29 ga watan Mayu, na wannan shekara ta 2023, zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki.

Najeriya – ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka na fuskantar ƙalubalen da suka haɗa da matsalar tattalin arziƙi da matsalar tsaro da kuma hauhawar farashin kaya.Da yawa na fatan Tinubu ya fara aiki a ƙasar ba tare da ɓata lokaci ba.

Leave a Reply