
Romero mai shekara 34 wanda yarjejeniyarsa ta kare a karshen watan Yuli, ya yi kaka shida a Old Trafford a matakin mataimakin David de Gea.
Wasa na karshe da dan kasar Argentina ya yi wa United shine na daf da na karshe a Europa League da Copenhagen cikin Agustan 2020, wanda kungiyar Old Trafford ta yi nasara da ci 1-0.
Shine mai tsaron ragar Argentina da ya dade yana mata gola a tarihi, mai fafatawa 96 kawo yanzu.
Romero – wanda ya taimaka wa United ta lashe Europa a 2017 – ya koma a matakin mai jiran ko-ta-kwana karkashin koci, Ole Gunnar Solskjaer.
Daga Solskjaer ya maida hankali ga Dean Henderson wanda ya koma United daga wasannin aro da ya tsare ragar Sheffield United a 2020.
Romero, wanda ya ci FA Cup da kuma EFL Cup a United, ya tsare ragar kungiyar sau 39 kwallon bai shiga ragarsa ba a fafatawa 61 da ya yi mata.
Venezia tana mataki na 17 a kasan teburin Serie A na bana, mai maki biyar daga fafatawa bakwai a babbar gasar Italiya.