Guda daga cikin masu zawarcin kujerar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar APC Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, A A Zaura, yace idan za’a mayar da kujerar shugabancin kasar nan zuwa ga shiyyar kudu, to kuwa Jagoran Dattawan jam’iyyar na kasa Alhaji Bola Ahmed Tunubu, shine mutumin da ya fi kowa cancantar ya gaji kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A.A Zaura wanda ya fadi hakan yayin da yake amsa tambayoyin manaima labarai game da rade raden da akeyi cewa ya dauko gabarar tallata takarar da Tunibun zai tsaya na neman tsayawa takarar shugabancin kasar nan, yayi bayanin cewa kyakyawar alakar da take tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Lagos dangan tace ta tun tale-tale gabanin siyasa ta sake hada su.
Acewar Zaura siyasarsa ba ta ko a mutu ko ayi rai bace ko karbar ragamar iko ta kowane irin hali, abinda ya fi baiwa fifiko yafi shine wanda yazo dai dai da muradun al’ummar jihar nan.