Kungiyar AC Milan ta sanar cewar Theo Hernandez ya kamu da cutar korona, bayan kammala wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya da ya yi wa Faransa.
Mai tsaron bayan Faransa ya buga wasan karshe a UEFA Nations League a Italiya, wanda ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga a karawar da suka ci Belgium da lashe kofi, bayan doke Sifaniya.
”Hernandez ya kamu da cutar korona, bayan buga wa Faransa tamaula, An sanar da dukkan jami’an lafiya, kuma dan wasan na cikin koshin lafiya” kamar yadda Milan ta saanar a Intanet.
Hernandez shine na biyu da ya kamu da annobar a tawagar Faransa, bayan dan kwallon Juventus, Adrien Rabiot wanda bai buga karawar karshe ba, bayan da ya kamu da cutar ranar Asabar.
Hernandez daya ne daga kashin bayan Milan a bana, bayan da ya buga mata dukkan fafatawar da ta yi a kakar nan, kuma killace kai da zai yi ka iya kawo koma baya ga kungiyar.
Kungiyar da Stefano Pioli ke horar wa tana ta biyu a teburin Serie A, za kuma ta kece raina da Hellas Verona da kuma Bologna a wasanninta na gaba, sannan ta buga Champions League da za ta ziyarci Porto.