Taƙaddama ta kaure kan batun miƙa mulki a Zamfara

Taƙaddama ta ƙaure tsakanin gwamnatin APC mai barin gado da kuma ta jam’iyyar PDP mai zuwa a jihar Zamfara, bayan zargin cewa ƙananan kwamitocin karɓar mulki na gwamati mai jiran gado na wuce gona da iri.

Gwamnatin jihar ta yi zargin cewa ƙananan kwamitocin na zuwa ma’aikatun gwamnati suna yin bincike tare da karɓar bayanai, wanda a cewar ta abu ne da bai dace ba kuma ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki.

Gwamnatin APCn ta ce abubuwan da kwamitocin ke yi yi tamkar ‘kafa gwamnati ne a cikin wata gwamnati’, inda ta buƙaci da su jira har sai an miƙa musu mulki.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Dosara, ya shaida wa BBC cewa ƙananan kwamitocin sun kasance suna bin ma’aikatu suna karɓar bayanai da gudanar da bincike tare da karɓar bayanan asussan ajiya na ma’aikatun domin yin bincike.

Dosara ya ce muddin kwmitocin ba su daina abin da suke yi ba, to hakan zai iya haddasa rikici, inda ya buƙace su da su bari har sai sun hau kan mulki.

“Duk bayanai da ake buƙata, ma’aikatun sun tattara tare kuma da miƙa wa kwamitin bayar da mulki, inda za su bai wa gwamna mai ci wanda shi kuma zai kira gwamna mai shigowa su zauna inda zai miƙa masa bayanan,” in ji Dosara.

Sai dai shugabannin kwamitin karɓar mulki na gwamnatin PDP mai jiran gado, ba su mayar da martani game da wannan zargi ba.

Amma Alhaji Muhammad Kabir Janyau, mamba a ɗaya daga cikin ƙananan kwamitocin karɓar mulkin, ya ce takaicin barin mulki ne ke sa gwamnatin mai barin gado yin magiya.

Kabir Janyau ya ce tattara bayanai da miƙa su daga gwamnati mai barin gado zuwa gwamnati mai zuwa abu ne da aka saba yi wanda ana yin haka ne domin ita gwamnati mai zuwa ta san daga ina za ta fara.

Ya ce watakila suna tsoron irin ayyukan da suka aiwatar da suka saɓa doka ne.

Irin wannan sa-in-sa da ke faruwa tsakanin gwamnati mai barin gado da mai jiran gado a jihar Zamfara na faruwa a wasu jihohin Najeriya musamman a wajen da mulki ya kuɓuce wa wata jam’iyya zuwa wata.

Ko a kwanakin baya ma, an samu irin wannan takun-sakar tsakanin gwamnatin NNPP mai jiran gado da kuma ta APC mai barin gado a jihar Kano.

Leave a Reply