Suyudi Isah Jibril Bichi ya zama Shugaban Guarantee Radio

Hukumar gudanarwar Gidan Radio Guarantee dake Kano, ta amice da nada Suyudi Isah Jibril Bichi amatsayin sabon shugaban      tashar.
Cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Manajan gudanarwa na tashar Abdul’Aziz Habib mai kwanan wata 21-10-23, tace nadin      yafara aiki nan take.
Sanarwar ta bukaci dukkanin Ma’aikata da shugabannin sassa na tashar dasu baiwa Sabon shugaban hadin kai domin dawo da martabar    tashar.
Kafin wannan nadi, Suyudi Bichi shine shugaban sashin shirye shirye na gidan Radio Guarantee.


Suyudi Isah Jibril Bichi, yayi Diploma a fannin aikin Jarida a Kwalejin fasaha ta Jihar Kano, ya kumayi Digirinsa na farko a fannin na aikin Jarida a Jami’ar Open University, inda yake da kwarewa ta shekaru masu yawa a aikin Jarida.
Bichi ya halarci kwasa kwasai a fannoni daban daban a aikin Jarida a ciki da wajen Jihar Kano.

Leave a Reply