Subul-da-bakan Tinubu ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya

‘Yan Najeriya sun shafe dare har zuwa wayewar garin wannan Larabar suna ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta dangane da wasu kalamai ko subul-da-baka da ɗan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a wurin yaƙin neman zaɓensa.

A jiya Talata ne Bola Tinubu ya kaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda  Shugaba Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka halarta. 

Sai dai a jawabinsa lokacin da ya hau dandamali ya yi wasu kalamai da wasu ke gani subul-da-baka ne.

Irin wadannan kalamai su ne wasu ‘yan Najeriya suka rinka watsawa a shafukan sada zumunta, wasu na amfani da kalaman zolaye, wasu kuma na cewa wannan katoɓara alamomin gazawa ce.

Kusan abu biyu ne suka ja hankalin ma’abota shafukan sada zumunta da kuma mutanen da suka bibbiya yadda gangamin ya kasance a garin Jos.

Akwai kuskure da ɗan takarar Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen kiran sunan jam’iyyarsu ta APC, inda aka jiyo ɗan takarar na ambato harufa biyu na babbar jam’iyyar adawa wato PDP, inda ya ce “PD…” amma daga bisani ya gyara ya ce “APC”.

Wannan kuskure ko subul-da-baka da Tinubu ya yi ya ja hankali sosai, inda mutane suka yanko daidai wajen suna ta sake wallafawa da takfa muhawara a kai.

Wasu ma sun haɗe sunan suna cewa ko dai Najeriya ta yi sabuwar jam’iyya ce ta “PDAPC”.

Duk da cewa Tinubu ya yi wasu kura-kurai a wajen yaƙin nema zaɓensa, akwai kuma batutuwa masu muhimmanci da ya taɓo, tare da alkawarta shawo kansu da zaran ya kasance mai nasara a zaɓen 2023.

Mista Bola Tinubu ya lissafo mafi yawan matsalolin da ke damun Najeriya, ciki har da karancin abubuwan more rayuwa da durkushewar masana’antu da rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Sannan ya yi alwashin magance su ta hanyar hada kwararru kuma gogaggu a cikin gwamnatinsa idan ya samu nasarar kafawa.

Ya ce: “Mu a jam’iyyar APC da yardar Allah mun yi wa ‘yan Najeriya alkawarin yin shugabanci nagari a karakashin wannan yunkuri na farfadowa ko sabunta fatan alheri a zukatan al’umma, sakamakon goyon bayan da kuke ba mu. Za mu hada ayarin jarumai don ciyar da kasa gaba”.

Kazalika, ɗan takarar shugaban kasar  ya caccaki abokan hamayyarsa musamman ma na jam’iyyun adawa da ke gaba-gaba, wani lokaci har da kiran suna yana gugar-zana, yana cewa ba su san hanya ba, ballantana su yi wa wani jagora.

Haka zalika da dama cikin ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi jawai sun nuna suna da kwarin gwiwa APC za ta kai labari a zabe mai zuwa.

Amma Shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya shawarci ‘yan jam’iyyar da kada su shagala, su bari mulki ya ruɗe su, su yi wa jam’iyya aiki idan suna so su ga alheri:

Ya ce: “Kasancewa a kan karagar mulki ba ya sa a dawwama a kan mulki. Ba zai hana faduwa ba idan ba mu dage mun yi abin da ya kamata mu yi da zai ma samu karbuwa a zukatan masu kada kuri’a ba.

Wannan ne ya sa nake jaddada cewa mu kasance masu himma. Mu hada kai ta yadda za mu gudu tare mu tsira tare,” in ji Abdullahi Adamu. 

One thought on “Subul-da-bakan Tinubu ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya

  • November 16, 2022 at 5:20 pm
    Permalink

    Allah ya kyauta

    Reply

Leave a Reply